Home Siyasa Zaɓen fidda-gwani: An kama koodinetocin Binani yayin raba wa daleget kuɗaɗe

Zaɓen fidda-gwani: An kama koodinetocin Binani yayin raba wa daleget kuɗaɗe

0
Zaɓen fidda-gwani: An kama koodinetocin Binani yayin raba wa daleget kuɗaɗe

 

An kama wasu koodinetoci biyu na wata ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa, Aishatu Dahiru, wacce a ka fi sani da Binani yayin da suke raba makudan kuɗaɗe ga daleget ɗin jam’iyyar APC gabanin fara zaɓen fidda-gwani na gwamna da za a yi a daren yau.

Ana kallon Binani wacce ke wakiltar Adamawa ta tsakiya a majalisar dattawa a yanzu a matsayin ƴar takara mafi ƙarfi a takarar gwamna a jihar.

Wakilan da suka zanta da Daily Nigerian sun ce ƴar majalisar ta yi alƙawarin ninka kuɗaɗen da abokan takarar ta su ka raba wa daleget, inda da yammacin yau ƴan barandan Sanatan suka fara tuntuɓar wakilan zaɓe domin cika alkawuran Binani.

Wasu da dama daga cikin ‘yan jam’iyyar da ba wakilai ba, an ce su ma sun shiga kasuwar ne domin samun nasu kason.

An kama wasu mutane biyu da har yanzu ba a tantance ko su waye ba da misalin karfe 8 na dare, yayin da rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro suka far wa daya daga cikin wuraren da ake hada-hadar raba kuɗaɗen.

Baya ga mutanen da aka kama da kuma kudaden da aka ƙwato, an kuma samu foma-fomai na alkawari da cikakkun bayanan wakilan a wajen.

Tuni dai a ka kai mutanen biyu da aka kama zuwa ofishin CID na ‘yan sandan Adamawa tare da kayan da s ka same su da su.

Ba a samu jin ta bakin kakakin ƴan sandan Adamawa domin jin ta bakinsa ba.