
Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya bayyana wata mata, Farfesa Kaletapwa Farauta, a matsayin mataimakiyar takararsa a zaben 2023, a karkashin jam’iyyar PDP.
Fintiri ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar war a Yola a yau Laraba, inda ya ce Farauta, wacce a halin yanzu ita ce Shugabar Jami’ar Adamawa, Mubi, an zaɓo ta ne bisa gaskiya, rikon amana, da kuma aiki tuƙuru.
Ya ce ana sa ran za ta iya sauke nauyin da za a ɗora mata tare da taka tsantsan da tsoron Allah, baya ga aikin da take yi na kula da gida a matsayin ta na uwa.
” An zaɓe ta ne sakamakon tunani da lissafi mai zurfi, musamman na buƙatar tafiya da mata ta hanyar bai wa ko wanne jinsi hakkinsa,” in ji shi.
A nata jawabin, Farauta, wacce ta bayyana zaɓen na ta cewa da ga Ubangiji ne, ta godewa MFintiri da kuma jam’iyyar PDP da suka zaɓe ta a matsayin wacce ta cancanta.
Ta tabbatar da yin aiki cikin biyayya, aminci, sadaukarwa, da tsoron Allah.
“Za mu yi aiki tukuru don tabbatar da nasara ga jam’iyyar a duk zabukan da za a yi nan gaba,” in ji ta