
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilan da suka sanya shi tube jar hular Kwankwasiyya da yayi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da akai a fadar Gwamnatin Kano, inda yace daya daga cikin dattawan jam’iyyar Alhaji Bashir Tofa ne ya yi masa kyautar hula kuma ya nemi ya ajewa a Kwankwaso hular sa.