
Daga Monrobiya babban birnin kasar Laberiya, hukumar zabe mai zaman kant, ta ayyana tsohon dan wasan kwallon kafar kasar George Weah a matsayi wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a ranar talatar da ta gabata.
An gudanar da sabon zaben shugaban kasar ta Laberiya ne, bayan da shugaban kasar me ci Ellen Johnson Sirleaf,ta kammala wa’adi na biyu a mulkin ta. Ita dai Sirleaf ta zama shugaban kasar ne tun a shekarar 2006, yayin da take kammala wa’adinta na biyu a wannan shekarar.
Ba wannan ne karon farko da George Weah yayi takarar shugaban kasa a Laberiya ba, ko a zaben da ya gabata ya kara tare da shugaban kasar mai ci Ellen Johnson inda ta kayar da shi a lokacin da take neman wa’adin mulki na biyu.
Wannan ta baiwa Weahdamar sake dawowa neman shugabancin kasar, inda ya samu nasara a wannan karon. Weah dai ya samu karbuwa musamman a tsakanin matasan kasar a matsayinsa na tsohon zakaran kwallon kafar kasar da ya fito da ita a idon duniya, musamman a shekarun 1996.
Tuni shugaba mai barin gado, kuma mace ta farko da ta zama shugabar kasa a yankin Afurka ta yamma Ellen Johnson Sirleaf ta taya George Weah murnar lashe zaben, ta kuma yabawa al’ummar kasar yadda suka fito suka yi zabe lafiya ba tare da tashin tashina ba.
Laberiya a matsayin kasar da ta sha fama da yaki za’a iya cewar ta hau turbar demokadiyya dodar a yammacin Afurka.