
Aƙalla mutane 44 ne su ka mutu sakamakon wata girgizar ƙasa da ta afku a tsibirin Java na Indonesia a yau Litinin.
Adam, kakakin karamar hukumar Cianjur a yammacin Java, ya shaida wa AFP cewa wannan adadi ne na wucin gadi ne saboda ba’a kai ga tantance adadin ba, inda gidaje da dama suka lalace.
Girgizar ƙasar mai karfin maki 5.6 a ma’auninta ta afku ne a tsibirin Java na kasar Indonesia a ranar Litinin, inda ta kashe mutane da dama tare da lalata gine-gine da kuma haddasa zabtarewar kasa.
Babban jami’in da ke yankin yammacin Java da girgizar kasar ta fi kamari, ya ce an kidaya wadanda suka mutu a asibiti daya kadai, ba tare da bayar da takamaiman adadi ba, yayin da wasu mutane da dam suka makale a wasu kauyuka da har yanzu ba a kai ga kwashe su ba.
Ya ce ƴan uwan wadanda lamarin ya rutsa da su sun taru a asibitin Sayang da ke garin, ya kuma yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa saboda har yanzu mazauna kauyukan da ke wajen garin na cikin makale.