Home Labarai Gobara: Mutane 3 sun rasu, shaguna 100 sun ƙone a kasuwar ƴan tumatur a Kano

Gobara: Mutane 3 sun rasu, shaguna 100 sun ƙone a kasuwar ƴan tumatur a Kano

0
Gobara: Mutane 3 sun rasu, shaguna 100 sun ƙone a kasuwar ƴan tumatur a Kano

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar yau Asabar a kasuwar Tumatur ta Badume da ke karamar hukumar Bichi ta jihar Kano ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane uku.

Sama da rumfuna 100 sun ƙone ƙurmus a gobarar.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa gobarar ta tashi ne daga wata rumfa dake tsakiyar fitacciyar kasuwar a kauyen.

Da ya ke bayyana lamarin, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi ya bayyana cewa hukumar ta samu kiran gaggawa da ga wani Ibrahim Tsalha da misalin karfe 3:30 na safiyar yau Asabar.

Ya kara da cewa, a lokacin da aka karɓi kiran na gaggawa, an yi gaggawar tura tawagar ceto zuwa wurin, inda wasu mutane uku da ba a san ko su waye ba, mace daya da maza biyu ciki har da wani dattijo mai bukata ta musamman, su ka makale a wani shago.

PRO ɗin ya bayyana cewa, an fito da wadanda lamarin ya rutsa da su ne a sume kuma daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu.

Ya ƙara da cewa, kimanin rumfuna dari ne su ka kone gaba daya, yayin da rundunar ta yi nasarar kashe gobarar domin kaucewa yaduwa zuwa sassan kasuwar.

Yusuf ya ce har yanzu ana gudanar da bincike kan musabbabin faruwar lamarin.

Ya kuma bukaci jama’a da su yi amfani da na’urorin kashe gobara da na lantarki tare da kiyayewa domin gujewa afkuwar gobara.