
Hukumar Kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA ta haramta wa masu hayar babur mai ƙafa uku, wanda a ka fi sani da adaidaita-sahu a jihar, bin wasu manyan tituna.
Dokar za ta fara aiki ne daga gobe Laraba, 30 ga watan Nuwamba, 2022.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan da ta samar da manyan motocin haya da za su maye gurbin adaidaita-sahu domin ɗaukar al’umma zuwa wasu sassan cikin birnin jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar ta KAROTA, Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa ya sanya wa hannu a jiya Litinin a Kano.
Sanarwar ta ce an haramta wa direbobin Adaidaita-sahun bin titunan Amadu Bello zuwa Gezawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta tanadi manyan motocin sufuri domin sauƙaƙawa al’umma bin waɗannan hanyoyi.
Gwamnatin ta ƙara da cewa za ta sanar da ranar da matuƙa Adaidaita Sahun za su daina bin wasu manyan titinan da zarar ta kammala samar da dogayen motocin da al’umma za su yi amfani da su.