
Gwamnatin jihar Kano ta hana yin hayar babur mai ƙafa uku, wanda a ka fi sani da adaidata sahu bayan ƙarfe 10 na dare.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar a yau Litinin.
Sanarwar ta ce an dauki matakin ne a ƙarshen taro kan tsaro a jihar, a ci gaba da yunkurin gwamnati na magance matsalolin rashin tsaro.
Ya kuma yi kira ga masu tuka adaidai ta shahu da su bi dokar da gwamnatin ta kafa, don gujewa fushin hukuma.
Ya ƙara da cewa dokar kuma za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis na wannan watan da muke ciki.