
Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta ce gwamnatin taraiya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur a karshen watanni ukun farko na 2022.
Ministar ta baiyana hakan ne a ranar Litinin a wata ganawa da ta yi da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a zauren majalisar, kamar yadda jaridar Guardian ta rawaito.
Ahmed ta ce cire tallafin a kowane lokaci a wannan shekara na iya kara taɓarɓarewar hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Ta ce: “Mun gano cewa a zahiri, har yanzu ana samun hauhawar farashin kayayyaki kuma cire tallafin zai ƙara dagula lamarin da kuma sanya karin wahalhalu ga ‘yan kasar.
“ Shugaban kasa ba son yin hakan ya ke ba. Abin da mu ke yi a yanzu shi ne ci gaba da tattaunawa da tuntubar juna ta fuskar samar da matakai da dama.
“Daya daga cikin wadannan sun hada da kaddamar da aikin tace matatun man fetur da ake da su da kuma samar da sabbi waɗanda za su rage yawan shigo da man fetur cikin kasar nan.
“Saboda haka, mu na buƙatar mu koma Majalisar Dokoki ta ƙasa domin a gyara kasafin kuɗin da kuma samar tanadin wani tallafin na man fetur cikin kasafin daga ranar 22 ga Yuli zuwa duk lokacin da muka amince ya dace da fara cirewa gaba daya.”