
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bukaci al’ummar da aka kai wa hari kwanan nan a karamar hukumar Alkaleri da su tashi su dauki makamai su kare kansu daga ƴan bindigar.
Daily Trust ta rawaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a jiya Alhamis a fadar Hakimin Yelwan Duguri, Alh Adamu Mohammed Duguri a ziyarar da ya kai kauyen Rimi, Gwana da Yalwan Duguri domin jajanta wa wadanda ‘yan fashin daji suka kai wa hari.
Ya ce ba za a yarda da hare-hare kuma dole ne a dakatar da shi ko ta yaya.
“An san ku mazaje ne, kada ku bari waɗannan miyagun abubuwa su mamaye ku, ku kare ƙasarku, ku kuma ƙwaci ƴancin ku. Ku tashi ku dauki makami domin ku kare kanku,” inji shi.
Gwamnan ya shawarci jama’a da su binciko mutanen cikin da ke hada kai da ‘yan bindigar, musamman wadanda ke aiki a matsayin masu kai musu tsegumi, inda ya kara da cewa masu laifin ba za su iya yin aiki ba tare da masu kai musu tsegumi ba.
Da yake mayar da martani, Hakimin Yelwa Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri, ya ce mutane 20 ne aka kashe a kauyen Rimi a lokacin hare-haren kuma yunkurinsu na kaiwa Kafin Duguri ya ci tura yayin da mutanen kauyen suka tashi domin kare kauyen.