
Daga Ado Abdullahi
Muna zaune akan kujera bayan mun yi sallama an shigo da mu cikin wani matsakaicin falo kenan. Falon ba wai wani irin mai ƙyale-ƙyalen nan ba ne irin na alfarma. Ba dai za ka ce yadda aka shirya kujerun ɗakin za su ja hankalin mai kallo ba, duk da ƴan boko ka iya cewa kujerun sun yi ‘matching’ da launin labulen ɗakin. Ba kuma za ka raina da kimarsu ba wato dai abin ‘mutawassuɗi’ ne. Ma’ana dai kai da gani kasan an nuna tsabagen ‘zuhudu’, wato ba a zurfafa wajen nuna akwai abin duniya ba.
Hakanan babu irin ƙaton hoton mai gidan a maƙale a bango ko wata ƴar kwana ko kusurwar ɗakin. Wato dai babu irin burgewar nan ta ƴan birni, wacce za ta nuna ka shigo falon wani babban mutum.
Mun ɗan yi jira na ƴan mintoci, can sai hadimin gidan ya ce,
“Ga Mallam nan shigowa”.
Wata ƙofa muka ga an buɗe daga cikin gida, ai kuwa Mallam ne ya shigo falon da muke a zaune. Bamu san lokacin da muka miƙe tsaye ba, tare da miƙa masa hannu bayan ya fara miƙo mana hannu tare da yi mana wani irin salihin murmushi wanda da gani ka san har zuci murmushin imani ne.
“Ya ya za ku miƙe tsaye don na shigo? Ai babu kyau musulunci bai koyar da haka ba”.
Haka ya faɗi cikin murmushi tare da yi mana barka da zuwa a lokaci guda. Duk da haka bamu zauna ba sai da muka jira zamansa duk don girmama babba.
Ni dai sai naji kamar na manta wannan hadisi a lokaci guda ina mamakin wane irin ɗan siyasa ne wannan da riƙo da ayyukan addini haka sau da ƙafa? Ni dai duk abin da muka tattauna a wannan rana babu abin da nake tunani irin wannan wa’azi mai ratsa jiki daga wannan malami kuma ɗan siyasa wanda ya yi takarar gwamna har sau biyu a jihar da tafi kowace jiha yawan al’umma.
Lallai Mallam Salihu Sagir Takai ya cancanci a kira shi Mallam. Mutum ne mai fara’a, son jama’a ƙaunar addini, kawaici da mutuntaka. Idan kuna tattaunawa ta siyasa za ka fahimci kusan ya fika sanin abin da kake neman bashi shawara a kai. Mutum ne ma kaifin basira da nutsuwa. Allah Ya bashi haƙuri da juriya. Hakanan mutum ne mai ƙwazo, gaskiya, riƙon amana da kishin cigaban musulunci.
Mallam Salihu Sagir Takai a lokacin da yake a ma’aikatar ruwa a zamanin mulkin Malam Ibrahim Shekarau ya jagoranci aikin gina matatar ruwa wacce Kano ba ta taɓa samun irinta ba. Mai bayar da ruwa lita milyan 150 a kullum. Aikin da kowa ya shaida ya tafiyar dashi bisa amana da ƙwazo.
Lallai a wannan aiki wanda aka kashe zunzurutun kuɗi har Naira bilyan 5.6. Baya kammala wannan aiki, Mallam Salihu ya dawowa da gwamnatin Kano da rarar kuɗi sama da Naira Milyan 200 a matsayin cewar sun yi yawa a kuɗin da aka bayar don gudanar da wannan aiki.
Akwai misalai irin waɗannan da zamu kawo su nan gaba na gaskiya, adalci, riƙon amana da ƙwarewa na Mallam Salihu Sagir Takai. Gami da hujjoji masu ƙarfi da zasu tabbatar da a yanzu dai a Kano babu wanda ya cancanci zama gwamna Kamar Mallam Salihu Sagir Takai.