
Tsohon Mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya rasa tikitin takarar jam’iyyar APC na majalisar wakilai a mazaɓar Gaya/Ajingi/Albasu ta jihar Kano.
Ahmad ya fafata da ɗan majalisa mai ci a mazaɓar, Mahmud Gaya.
Sakamakon da aka sanar a daren Juma’a ya nuna cewa Ahmad ya samu kuri’u 16 kacal, yayin da Gaya ya samu kuri’u 109.
Yanzu dai Gaya ya samu tikitin jam’iyya mai mulki na neman wa’adi na biyu a zaɓen 2023.
Ahmad ya bar gurin da ake yin zaɓen na fidda-gwani tun kafin a kammala shi.
Daga nan sai ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa: “A matsayina na mai son tsayawa takara, na bar wurin zaben fidda-gwani na mazabar Gaya, Ajingi da Albasu na tarayya, saboda barazanar rashin tsaro a kan wakilanmu. Idan a na son a yi zaɓe sahihi to kada a yi amfani da ƴan daba,”