
Rahotanni da ga Jihar Zamfara sun baiyana cewa ƙasurgumin ɗan ta’addan nan, Bello Turji, wanda ya ke fashin daji da garkuwa da mutane a Arewa-Maso-Yammacin Nijeriya, ya tsere da ga sansanin da ya kafa sakamakon luguden wuta da ga dakarun Nijeriya.
A ƴan kwanakin nan ne dai rundunar sojin Nijeriya ta tarwatsa sansanonin ƴan ta’adda a hare-haren jiragen yaƙi a Zamfara.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa majiyoyi sun baiyana cewa hare-haren jiragen yaƙin ne ya tilastawa Turji da mayaƙan sa tserewa da ga dajin Fakai da ke Ƙaramar Hukumar Shinkafi zuwa kudancin Zamfara.
Majiyoyin sun ce an hango ƴan ta’addan su ma kafa tantuna a dajin Gando da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum.
Kusan ma dai yan ta’addan me ke riƙe da garin, inda ƴan garin da abin ya rutsa da su ke cewa ƴan rashin dajin sun kakkafafa bukkoki kuka a babura su ke tafiya, yayin da wasu kuma su ke tafiya a kafa tare da dabbobin da su ke ƙwacewa al’umma.
Jaridar ta ƙara da cewa ba ta samu damar samun kakakin rundunar ƴan sanda na Zamfara, SP Muhammad Shehuba yayin haɗa rahoton.