Home Lafiya Haukan cizon kare na kashe ƴan Nijeriya 55,000 a shekara — USAID

Haukan cizon kare na kashe ƴan Nijeriya 55,000 a shekara — USAID

0
Haukan cizon kare na kashe ƴan Nijeriya 55,000 a shekara — USAID

 

Ciwon haukan kare na zama sanadin kashe mutum 55,000 duk shekara a Najeriya, yayin da karnuka masu ciwon hauka suka kai kimanin kashi 94 na dabbobin da aka tabbatar suna yada cutuka ga mutane.

Mataimakiyar Daraktan kula da lafiya a Hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) a Najeriya, Mieko Mckay ce ta bayyana haka kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito yayin kaddamar da Tsararren Shirin Kakkabe Mummunan Ciwon Haukan Kare da Karnuka ke haddasawa a Najeriya.

An shirya taron ne gabanin Ranar Tunawa da Ciwon Haukan Kare ta bana da ake gudanarwa duk 28 ga watan Satumba. Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya a Najeriya shi ma a nasa jawabi, ya ce a baya-bayan nan an samu irin wannan yaduwar ciwon haukan kare a jihohin Gombe da Enugu.

Karamin ministan noma da raya karkara, Mustapha Shehuri ya ce an bullo da shirin ne don ya taimaka wa Najeriya wajen cimma burinta na kakkabe ciwon haukan kare nan da shekara ta 2030