Home Kanun Labarai Hukumar EFCC na tsare da tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya lokacin Jonathan

Hukumar EFCC na tsare da tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya lokacin Jonathan

0
Hukumar EFCC na tsare da tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya lokacin Jonathan
Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya Anyim Pious Anyim

Hukamar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC na tsare da tsohon sakataren Gwamnatin tarayya zamanin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, Mista Anyim Pious Anyim a ofishinta da ke babban birnin tarayya Abuja.

Tsohon sakataren Gwamnatin na fuskantar tuhuma ne kan almundahana da makudan kudade kan bikin cikar Najeriya shekaru 100 da haduwa tsakanin kudu da Arewa, wani kasaitaccen bikin da aka gabatar a birnin Abuja.

Idan za’a iya tunawa, Majalisar tarayyar Najeriya ta bayar da shawarar a gabatar da Mista Anyim a gaban kuliya, bisa zargin facaka da ake masa a yayin wannan kasaitaccen biki a Abuja, a wancan lokacin.

Ana dai zargin Mista Anyin da mukarrabansa a lokacin wancan biki, sun yi watandar sama da Dalar Amurka biliyan 18, sannan suka yi watandar wasu filayen da suka mallakawa kansu da makusantansu.