
Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa, FRSC, ta ce ba ta daukar ma’aikata, ta kuma gargadi masu neman aiki da su guji faɗa wa hannun ƴan damfara.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in kula da wayar da kan jama’a na hukumar, CPEO, Bisi Kazeem, ya fitar a yau Juma’a a Abuja.
Kazeem ya ce wannan bayanin ya zama dole ne biyo bayan yunƙurin da wasu da ake zargin ƴan damfara ke yi na zamba ga masu neman aiki ko masu daukar nauyinsu.
“An jawo hankalin hukumar FRSC ga wallafe-wallafen da ke neman yaudarar jama’a kan cewa hukumar mu na ɗaukar aiki.
“Wannan hanyar ita ce ta sanar da jama’a cewa FRSC tana nan, ba ta daukar ma’aikata ba kuma babu wani shiri na yin hakan,” in ji shi.
Kazeem ya ce shugaban FRSC na rikon kwarya, Dauda Biu, yana gargadin masu neman aiki da sauran jama’a da su yi watsi da labaran karya da yaudara.
Biu ya ce hukumar na amfani da tsari a bude yayin da ta ke daukar sabbin ma’aikata.