Home Labarai 2023: Idan na ci zaɓe dole na cire tallafin man fetur — Obi

2023: Idan na ci zaɓe dole na cire tallafin man fetur — Obi

0
2023: Idan na ci zaɓe dole na cire tallafin man fetur — Obi

 

 

Ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi, ya ce idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban kasa a 2023, gwamnatinsa za ta kawo karshen dogaro da mai da kuma tallafin man fetur.

Obi ya bayyana haka ne a taron Gamayyar Kungiyoyin Goyon-bayan Peter, CPO, da aka gudanar a babban ɗakin taro na kasa da ke Abuja.

Ya ce: “Na sha faɗa cewa duk da cewa akwai bukatar samar da hanyoyi na ƙarfi da za a bi wajen yaki da rashin tsaro, akwai kuma bukatar a gaggauta magance talauci da tabarbarewar zamantakewa da tattalin arziki da ke kara ta’azzara rikicin.

“Ba za ta yiwu a samu kashi 33% na rashin aikin yi ba, yara miliyan 18.5 da ba sa zuwa makaranta da kuma talakawa miliyan 100, a Najeriya kuma mu sa ran mu yi barci da idanunmu biyu.

“Kudaden da Najeriya ke rabawa na man fetur ya kare! Yanzu muna kashe kuɗi mafi yawa a kan biyan kuɗaɗen ruwa na bashin fiye da yadda muke samu daga mai! Yanzu Najeriya ta fi kashe kudaden tallafin da ake samu a man da ake tacewa daga kasashen waje fiye da yadda take samu daga siyar da danyen mai!

“Idan muka ci gaba, dole ne mu nemi hanyoyin da za mu bi wajen ciyar da Najeriya gaba. Dole ne mu kawo karshen laifin da ake kira tallafin man fetur,” in ji shi.