
Daga Ado Abdullahi
Aikin jarida na binciken ƙwaƙwaf aiki ne da ƴan jaridu kan shafe kwanaki, watanni, wani lakaci har shekaru domin bincikar wata badaƙala da ta afku a gwamnati ko wata ma’aikata mai zaman kanta ko wani laifi da ake son dogon bincike a kai.
Manyan ƴan jaridu kan shiga wannan aiki mai haɗarin gaske, cin lokaci gami da jan kuɗi Aiki ne da ake yin sa ba da wasa ba. Kuma mutum kan tabbatar da gaskiyar aikin kafin ya bayyana shi ga al’umma.
Tabbas irin wannan aikin jarida ya yi nisa a ƙasashen waje musamman ɓangaren turawa waɗanda suka yi nisa a wannan fage. Amma hatta a ƙasashenmu na Afirika mun sami wani ƙwararren ɗan jarida daga ƙasar Ghana, wanda ya yi ƙoƙari wajen bankaɗo wasu badaƙala da wasu manyan jami’an gwamnatin ƙasar ta Ghana suka afka ciki.
Anas Armaya’u Anas ya sami lambobin girma masu yawa a ƙasar da ma yabo daga ko’ina cikin duniya. Hatta tsohon Shugaban ƙasar Amurka wato Barrak Obama ya yabe shi, inda ya nuna cewar Anas jarumi ne, mai hazaƙa wanda ya saka rayuwarsa cikin hatsari domin ceto al’umma daga sharrin masu karɓar cin hanci da rashawa.
Anas ya banƙado almundahana ta karɓar cin hanci da rashawa wacce ta saka aka tuɓe manyan alƙalan ƙasar kusan 13 da wasu ƙananan alƙalai 20 gami da korar sama da mutane 120 a ma’aikatar shari’ar ƙasar.
Dalilin bankaɗo wata badaƙala da Anas ya yi a hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Ghana, shugaban ƙasar ya rushe hukumar tare da korar shugaban hukumar. Haka nan Anas Armaya’u ya bankaɗo wata almundahana ta cin hanci da rashawa daga wani alƙalin wasan hukumar ƙallon Ƙafa ta duniya wato FIFA. Mutumin ɗan ƙasar Kenya wato Marwa Range. Wanda aka kama a wani faifan bidiyo yana karɓar cin hanci na wasu kuɗi na Dalar Amurka. Dalilin haka aka cire sunan Marwa Range daga cikin alƙalan wasan ƙwallon ƙafar ta duniya.
Anan Nijeriya kuwa muna da misali da dama na aikin jarida na binciken ƙwaƙwaf ba zamu taɓa mantawa da ƙoƙarin aikin Dele Giwa ba a zamanin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida.
Ko cikin ƴan watannin nan, mun ga inda aikin jaridar ya yi sanadiyyar ajiye muƙamin ministan ƙudi wato Kemi Adeosun. Saboda jaridar Premium Times ta bankaɗo badaƙalar yin amfani da takardar aikin yiwa ƙasa hidima ta bogi da ministan ta yi.
Babu mamaki ganin yadda Mallam Jaafar Jaafar Editan jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian ya fara binciken ƙwaƙwaf akan wata badaƙalar karɓar cin hanci da rashawa da gwamnan Kano wato Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya afka ciki. Haƙiƙa wannan aiki ba wai sabon abu bane a aikin jarida kamar yadda muka faɗi a sama. Sai dai a ce sabon abu ne a mu nan Arewacin Nijeriya. Wannan yasa abin ya zo da cece-kuce mai yawa.
Mallam Jaafar ɗin ya yi alwashin sakin fayafayen bidiyo kusan 15 domin tabbatarwa da jama’a wannan aika-aika. Ɗan jaridar ya yi iƙirarin cewar gwamnan ya karɓi maƙudan kuɗaɗe kimanin dalar Amurka miliyan 5 kwatankwacin kuɗi sama da naira Biliyan ɗaya da Miliyan 800. Waɗannan kuɗaɗe ana zargin gwamnan ya karɓa daga hannun ƴan kwangila ne a matsayin kafin alƙalami.
Yanzu dai ɗan jaridar ya fara sakin faifan bidiyo ɗaya kacal cikin goma sha biyar da ya alƙawarta. Kuma ya tabbatar da sahihancinsu domin ya ce masana a kan harkar hotuna sun tabbatar da sahihancinsu kafin a fara saki ga al’umma.
Ita kuma gwamnatin jihar ta Kano ta bayyana aniyarta ta iza ƙeyar ɗan jaridar gaban ƙuliya manta sabo. Sai dai akwai babban abin tsoro ga gwamnan domin dai ɗan jaridar ya bayyana bai fito ba sai da ya shirya.Domin kamar yadda ya bayyana, ƴan kwangilar ne da kansu suka buƙaci aikin ɗan jaridar domin fallasa hauma-haumar gwamnan.
Lallai idan wannan badaƙala ta tabbata ga gwamna Ganduje to babu makawa zai ajiye muƙaminsa na gwamna ne ko kuma majalisar dokoki ta jihar ta tsige shi ba tare da ɓata lokaci ba. kuma a ƙarshe ya fuskanci shari’a bisa ga laifin da ya tafka na karɓar cin hanci da rashawa wanda ya saɓa da kundin tsarin mulkin ƙasar nan. Haka kuma ya saɓa da manufar shugaba Muhammadu Buhari na yaƙi da cin hanci da rashawa.
Lallai wannan aiki na Mallam Jaafar Jaafar abin a yaba ne, ya nuna jajircewa gami da rashin tsoro da rashin kwaɗayin abin duniya. Domin dai kamar yadda ya bayyana hirarsa da gidan radiyon BBC, manyan jami’an gwamnatin jihar ta Kano sun nemi ya zo a yi sulhu kafin ya saki faifan bidiyon. Sai dai ɗan jaridar ya yi kafiya akan hakan.
Ado Abdullahi
15-10-2018