
Hamshakin ɗan kasuwa kuma mai taimako, Alhaji Aminu Dantata da Abdulsamad Isyaku Rabi’u, mamallakin kamfanin BUA Group, sun haɗa tallafin sama da Naira biliyan daya ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa.
An bada tallafin ne a taron haɗa tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a jiya Asabar a birnin Dutse na jihar Jigawa.
Dantata da Abdulsamad kowannen su ya bada gudunmawar Naira miliyan 200, inda gwamnatin Jigawa ta bada Naira miliyan 250, sai kuma gwamnan Jihar, Muhammad Badaru, ya bada gudunmawar Naira miliyan 25.
Dantata, wanda ya samu wakilcin Alhaji Salisu Sambajo ya nuna damuwa kan yadda ambaliyar ruwa ta jefa al’umma cikin mawuyacin hali.
Ya kuma yi addu’ar samun Rahma ga waɗanda su ka rasu da kuma waɗanda ambaliyar ta raba su da mahallansu da gonakinsu.
A nashi ɓangaren, Gwamna Badaru ya gode wa wadanda su ka bada tallafin, inda ya hori kwamitin rabon tallafin da ya yi gaskiya da amana wajen rabon ga wadanda abin ya shafa.