
A ranar Juma’a ne kamfanin Dana Airline ya sanar da cewa zai ci gaba da gudanar da ayyukansa a ranar 9 ga watan Nuwamba.
Ememobong Ettete, Manaja a kamfanin Dana Airline ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da jami’in sadarwa na kamfanin, Kingsley Ezenwa ya fitar a Legas.
Hukumar kula da Zirga-zirgar Jiragen sama ta Ƙasa, NCAA, ce ta dakatar da lasisin sufurin jiragen sama, ATL, da kuma Lasisin Tashin Jirgi, AOC, tun daga ranar 20 ga watan Yuli.
Darakta Janar na Hukumar NCAA, Musa Nuhu, wanda ya bayyana dakatarwar, ya ce hukumar ta gano cewa kamfanin jirgin ya gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyansa da kuma gudanar da zirga-zirgar jiragen sama lafiya.
Ettete ya bayyana haka ne a cikin sanarwar da kamfanin ya fitar kan shirin dawo da shi bayan kammala binciken da hukumar ta yi.
Ya ce tantancewar da aka yi wa kamfanin jiragen sama, wani tsari ne na sake gyara da kuma garambawul, inda ya ce a kuma yi nasarar kammala shi.
Ettete ya ce an gudanar da cikakken binciken kuma kamfanin jirgin ya kuma sami sabbin jami’an gudanarwar da ke da cikakken iko.