
An kai Zainab Duke-Abiola, ɗaya daga cikin matan marigayi MKO Abiola, gidan yari na Suleja bisa zarginta da cin zarafin wata ‘yar sanda da aka bata ta zame mata dogari, Teju Moses.
A yau Juma’a ne rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja ta gurfanar da Duke-Abiola tare da ma’aikaciyarta Rebecca Enechido a gaban wata kotun majistare da ke zaune a gundumar Wuse.
A na tuhumar waɗanda ake zargin, wadanda ke zaune a Garki, Abuja, da laifin haɗa baki, yunkurin aikata kisan kai, da haifar da mummunan rauni ba tare da yi mata komai ba, cin zarafi da kuma cin mutunci da gangan da nufin kawo rashin zaman lafiya.
Sai dai wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.
Don haka mai shari’a Elizabeth Wonu, ta bayar da umarnin a tsare su a gidan gyaran hali na Suleja sannan ta ɗage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 5 ga Oktoba domin sauraren karar.