
Dan takarar Gwamnan jihar Kano a jamiyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai ya jaddada aniyarsa ta biyan ƴan fansho haƙƙoƙinsu da zarar ya yi nasara a zaɓen shekara ta 2023.
Yakasai, ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a jiya Litinin a Kano.
Ɗan takarar gwamnan ya bayyana cewar al’amarin fansho abu ne da ya ke buƙatar kulawa ta musamman, duba da cewa ma’aikata sun ƙarar da rabin rayuwarsu wajen hidimtawa gwamnati da al’umma, inda ya ce akwai bukatar a basu hakkokinsu.
A cewar sa, da waɗannan haƙƙoƙin ne ƴan fansho za su cigaba da tafiyar da al’amuran rayuwar su.
Ya kuma nuna damuwar sa dangane da yadda gwamnatoci ba su fiye kulawa da haƙƙoƙin ƴan fansho ba, inda ya ci alwashin idan har ya ci zaɓe a 2023, to kakarsu ta yanke saƙa.
Yakasai ya nuna cewa dama manufofin jam’iyyar PRP su ne a bunƙasa rayuwar talaka da kuma samar masa da walwala.