
‘
Wata budurwa mai suna Ilham Kabir Karaye ta shiga hannun ƴan sanda a Jihar Kano bayan da ta tsere da motar saurayinta a lokacin da ya kai ta zai sai mata shawarma a wani waje mai suna Shawarma Zone.
Tun da fari, Ilham ta kira saurayin nata ne da ya zo ya kai ta ya sai mata shawarma, inda tuni ya bazamo ya zo domin ya biya mata bukatar ta.
Da zuwan su wajen sayen shawarmae, sai saurayin nata ya bata kuɗi ya ce ta fita ta je ta sayo, amma sai Ilham ta dage cewa sai dai shi ya fita daga motar ya je ya siyo mata.
Fitar da ke da wuya, sai ta kira wani saurayinta, Mohammed Salisu, ya ce ya zo ya ja motar wani da ta ke bin kuɗi naira dubu 150.
Bayan Salisu ya zo ya ja motar, shi kuwa saurayin Ilham ɗin, ya fito daga Shawarma Zone cike da murnar cewa zai faranta wa sahibar ta sa, sai kawai ya ga wayam ba mota, lamarin da ya jefa shi cikin rudani.
Da saurayin ya kai ƙorafi Caji-ofis ɗin ƴan sanda, tuni su ka fara bincike, har su ka gano da kuma kamo Ilham tare da daya saurayin nata da ya tsere da motar
Da ƴan sanda ke tuhumar Ilham, sai ta ce ta yi hakan ne domin ta ja wa saurayin nata kunne sabo da yai mata alƙawarin zai bata Naira dubu 150 amma bai cika alkawarin ba.
Da ake tuhumar Salisu, wanda ya ja motar, ya ce Ilham ce ta kira shi ta ce ya ja motar, inda ya kai ta gidansu ya ajiye ta a unguwar Danbare a cikin birnin Kano.
Rundunar Ƴan 3, ta bakin kakakin ta, Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.