
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC, ta bayyana jam’iyyar APC da ‘yan takarkarunta a zaman wadan da suka lashe dukkan zabukan kananan hukumomin jihar 44 a zaben da aka gudanar ranar Asabar.
Shugaban hukumar zabe ta jihar Kano, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya bayyana sakamakon zaben ga manema labarai a jihar Kano yau Lahadi.
Farfesa Sheka yace Jam’iyyar APC ta kuma yi nasarar share dukkan kujerun kansiloli 484 na jihar da gagarumin rinjaye, a zaben da jam’iyyu 25 suka shiga ciki.
Ya kara da cewar, zaben wanda aka gudanar cikin lalama, yace an samu nasarar wannan zabe ne yadda aka samu dumbin mutane suka fito wannan zabe, sannan kuma jami’an tsaro sunyi aikinsu yadda ya dace.
“Jami’an tsarn da suka hada da ‘yan sanda, da na hukumar NDLEA da NSCDC da sauran dangin jami’an tsaro duk sun taimaka wajen gudanar da wannan zabe lami lafiya”
“Ina alfahari da cewar jam’iyyu 25 ne suka shiga cikin wannan zaben, kuma anyi zabe cikin tsanaki ba tare da wani tashin hankali ko yin magudi ba”
Shugaban hukumar zaben na Kano, ya bayyana cewar an dan samu jinkirin isar kayan zabe zuwa wasu mazabun, yace wannan ya faru sabida yadda aka sayo kayan zaben daga kasar Chana.
“Hukumar zabe ta karbi wasu kayayyakin zaben a ranar da aka fara zabe da misalin karfe 12:45, amma duk da haka anyi kokarin raba su zuwa mazabun jihar”
“Cikin gaggawa bayan mun karbi kayan zaben, muka shiga rarraba su da misalin karfe 4 na asubah, zuwa 11 mun kammala rarraba kayan zabe zuwa dukkan mazabu”
“A sabida haka, mun fahimci dukkan irin kurakuran da muka fuskanta a wannan zaben, mun gabatar da afuwarmu a irin matsalolin da aka fuskanta, a sabida haka zamu yi kokarin gyara dukkan kurakuran da muka fuskanta a wannan zabe, domin kaucewa sake aukuwar hakan anan gaba: A cewar Farfesa Sheka.
NAN