
A jiya Juma’a ne wata kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 28, Abdullahi Umar hukuncin ɗaurin watanni 33 a gidan gyaran hali, sannan ta ba da umarnin a yi masa bulala 40 sakamakon wulaƙanta kabari a jihar.
Umar wanda ke zaune a Sharada Quarters, Kano, ya bayyana a wani faifan bidiyo, ya na kwarara ashariya ga wani a wayar salula yayin da ya ke tsaye a kan wani kabari a wata makabarta, lamarin da ya jawo damuwa da Allah wadai a jihar.
Daga baya ne kuma sai rundunar ƴan sanda ta kama shi, kuma bayan bincike ta gurfanar da shi a gaban kotu.
Da ake yanke wa Umar hukunci, an tuhume shi da laifuka biyar da suka haɗa da haɗa baki, shiga waje don aikata laifi, tada hankalin jama’a, hassala al’umma da kuma yin amfani da yanar gizo ba bisa ka’ida ba, bayan ya amsa laifinsa.
Alkalin kotun, Malam Nura Yusuf Ahmad, ya yanke wa matashin hukuncin zaman gidan yari na watanni uku ko kuma biyan tarar Naira 5,000 bisa samunsa da laifin haɗa baki.
Ya kuma yanke masa hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan kaso ba tare da zaɓin tara ba saboda laifin shiga waje ya aikata laifi, da kuma ɗaurin watanni 18 a gidan kaso ba tare da zabin tara ba bisa tayar da hankali da kuma hassala al’umma.
An yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari ko kuma ya biya tarar N30,000 bisa laifin amfani da yanar gizo ya aikata laifi da kuma yi masa bulala 40.
Lauyan masu gabatar da kara, Aliyu Abideen, ya sanar da kotun cewa wani matashi ne ya kai ƙara a ofishin ƴan sanda na Sharada, Kano a ranar 13 ga watan Agusta.
Ya ce a ranar 9 ga watan Agusta, da misalin karfe 3:30 na rana, wanda ake tuhuma, tare da wani mai suna Mummunai, wanda yanzu haka ya tsere, sun kutsa kai cikin makabartar ƙauyen Maidille.
“Su biyun sun je kabarin mahaifiyar wani Abubakar Mai-Abinduniya kai tsaye saboda sun samu ƴar rashin fahimta, su ka yi fitsari a kabarinta su ka kuma ɗauki bidiyon abin da ya aikata,” Inji shi.
Abideen ya kuma ce daga baya wanda ake tuhuma ya wallafa bidiyon da aka naɗa a shafukan sada zumunta da suka hada da Facebook, YouTube da WhatsApp, wanda hakan ya janyo suka daga al’umma.
A cewar mai gabatar da kara, laifin ya ci karo da tanadin sashe na 120, 212, 341, 275 da 404 na dokar Shari’ar Jihar Kano.