Home Ƙasashen waje Karya dokar kulle: Firaministan Birtaniya ya tsallake tsige wa

Karya dokar kulle: Firaministan Birtaniya ya tsallake tsige wa

0
Karya dokar kulle: Firaministan Birtaniya ya tsallake tsige wa

 

 

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson ya tsallake rijiya da baya a kuri’ar da ƴan majalisar kasar suka kaɗa domin tsige shi ko kuma tabbatar da shi a karagar mulki.

Wannan dai na zuwa ne, bayan da ya samu kuri’u 211 daga ƴan majalisar da ke neman kasancewarsa a kan mulki, yayin da 148 su ka nemi a tsige shi.

Sakamakon na nufin Johnson ya tsallake rijiya da baya a kuri’ar amincewa ko kuma rashin amincewa da jam’iyyarsa ta masu ra’ayin rikau ta kawo.

A tuna cewa Johnson ya shiga matsala me bayan da a ka kama shi da laifin karya dokar kulle ta korona ta hanyar yin liyafa a Downing Street, hakan ya sanya ya zama Fira Ministan Birtaniya na farko da ya karya doka, inda ake ganin hakan ya haifar da nakasu ga martabarsa.

A ƙuri’un da masu ra’ayin riƙau su ka kaɗawa, magabata irin Margaret Thatcher da Theresa May duk da cewa sun sha da kyar, amma daga karshe sun yi murabus.

Bayan ya tsallake rijiya da baya a zaben na ranar Litinin, Boris Johnson zai iya ci gaba da zama shugaban jam’iyyar Conservative da kuma matsayinsa na Fira minista.

A karkashin dokokin yanzu, ba za a bar ‘yan majalisar masu ra’ayin rikau su sake gudanar da kuri’ar yankar-kauna ba har tsawon shekara guda.