
Ƴan ƙungiyoyin ɗariƙu, ƙarƙashin Inuwar Wayar da kan Ɗariƙa, sun baiyana aniyar su na tsunduma cikin siyasa a kakar zaɓe ta 2023 a Jihar Katsina.
Ƴan ɗariƙar sun kuma ci alwashin za a dama da su wajen zaɓo ɗan takara idan kakar zaɓe ta 2013 ta zo.
Shugaban ƙungiyar, Mallam Aminu Zango me ya baiyana hakan a yayin taron ƙaddamar da kwamitoci huɗu da za su ja ragamar ƙungiyar a jihar a jiya Lahadi.
Ya ce kashi 95 cikin 100 ma ƴan ƙungiyar matasa ne da su ka fito daga zawiyyoyi daban-daban.
Zango ya ce ƙungiyar ta ɗauki gaɓaran a dama da ita a siyasa ne “sabo da idan mu ka koma gefe mu ka zama ƴan kallo a siyasa to kamar muna cutar kan mu ne da ƴan ƙungiyar mu sabo da mu ya kamata mu san nagartar ƴan takarar da za su mulke mu.
“Kai da kake da hakkin zaɓar shugaba, to ya kamata kaima ka shiga siyasar domin ka samu masaniyar wanda ya kamata ka zaɓa.
“Amma kuma magabatan mu, malaman mu na zaure duk Basu san da haka ba.
“Su kawai abinda su ka sani shine a kawo musu shugaba kawai su bishi, sabo da su a lokacin su a kwai gaskiya da rikon amana kuma shugabanni ne na gari,” in ji shi.