
An tasa ƙeyar wani Musulmi daga cikin jirgin Southwest Airlines saboda wata fasinja ta ji ya ce “Insha Allah”.
Lamarin ya faru da wannan matashi Khairuldeen Makhzoomi dan shekara 26 a filin sauƙar jirage na Los Angeles International Airport a watan Afrilun wannan shekara.
Ya ce yana zaune kafin jirgi ya tashi yana waya da kawunsa da ke Bagadaza, kawun na bashi labarin labarin yadda ya yiwa tsohon shugaban majalisar ɗinkin duniya Ban Ki-moon tambaya a wajen wata walima a daren da ya gabata.
Shi dai yace a karshen maganarsu ya ce “Insha Allah”.
“Daga nan sai naga wata mata na yi min wani irin kallo, can kuma sai naga yan sanda sun zo kaina sun ce na tashi na fito daga jirgin,” Khairuldeen ya shaidawa CNN.