Home Siyasa 2023: Kotu ta bada belin Ciyaman da Sakataren PDP na mazaɓar Muhammad Abacha

2023: Kotu ta bada belin Ciyaman da Sakataren PDP na mazaɓar Muhammad Abacha

0
2023: Kotu ta bada belin Ciyaman da Sakataren PDP na mazaɓar Muhammad Abacha

 

 

 

Kotun majistire da ke zamanta a Nomans Land, karkashin mai shari’a Talatu Makama, a jiya Juma’a ta bada belin Ciyaman ɗin jam’iyar PDP, Umar Alhassan da sakataren jam’iyar, Auwal Muhammad, bayan da ta fara sauraron ƙarar.

Tun da fari, ƴan sanda ne su ka shigar da ƙarar Alhassan da Muhammad, bayan da Muhammad Abacha, ɗan takarar gwamna na ɓangare ɗaya a PDP a Kano, ya rubuta wa Babban Sufeton ‘yan-sandan Kasar nan koke, game da shugaban da sakataren jam’iyyar ta PDP na mazaɓar Fagge B.

Abacha ya rubuta koken ne bisa iƙirarin da su ka yi na cewa shi ba ɗan jam’iyyar PDP ba ne, sabo da bai karɓi katin jam’iyya ba, kuma ba sunansa a rijistar PDP na mazaɓar ta Fagge B.

A jiya Juma’a ne dai kotun ta fara sauraron karar da yan sanda suka shigar, inda bayan ta saurari ɓangarorin biyu, lauyan waɗanda a ke ƙara, ya roki kotun da ta bada belin su.

Sai dai kuma, ɗan sanda mai gabatar da kara, Nura ya yi doguwar suka kan buƙatar bada belin.

Bayan jin ɓangarorin biyu ne kuma sai mai Shari’a Makama ta amince da roƙon lauyan waɗanda ake ƙara, inda ta sa su a hannun belin a bisa sharuɗɗ guda biyu.

Sharaɗi na farko shi ne, kowannesu ya kawo mutum biyu da za su tsaya masa, inda sharaɗi na biyu kuma shine su bada jimillar kuɗi Naira Miliyan 1 kowannesu.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Satumba domin cigaba da shari’ar.

Tun da fari dai, ɗan takarar gwamna a PDP a Kano, Jafar Sani Bello ne ya yi ƙarar Muhammad Abacha a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a nan Kano, bisa zargin ya shiga zaɓen fidda-gwani na PDP har ya yi nasara a zaben, ba tare da ya cika ƙa’idojin jam’iya kamar yadda suke kunshe a cikin tanade-tanaden kudin tsare-tsaren ta ba.

Bello na ƙorafin cewa Abacha bai shaida wa mazaɓar sa ta Fagge B aniyar sa ta komowa jamiyar PDP tare da tabbatar da sunan sa ya shiga rijistar jamiyar a matakin mazabar tasa ta Fagge B ba.

Babbar kotun tarayyar dai zata fara sauraron shari’ar a ranar 14 ga Satumba.