Home Siyasa Kotu ta hana PDP dakatar da Wike

Kotu ta hana PDP dakatar da Wike

0
Kotu ta hana PDP dakatar da Wike

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin ta hana jam’iyyar PDP dakatarwa ko kuma korar Gwamnan Rivers, Nyesom Wike daga jam’iyyar.

Mai shari’a James Omotosho ya bayar da wannan umarni ne biyo bayan wani kudiri na gaggawa da gwamna Wike ya shigar a kan jam’iyyar PDP da manyan shugabannin ta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, Mista Wike, a cikin karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/139/2023, ya shigar a kan jam’iyyar PDP, kwamitinta na Ƙoli na kasa, NWC da kwamitin zartarwa na kasa, NEC.

Sauran wadanda suka shiga karar a ranar 2 ga watan Fabrairu sun hada da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu; sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Samuel Anyanwu, da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, a matsayin wadanda ake ƙara na 1 zuwa na 6.

Gwamnan na roƙon kotun da ta umurci dukkan bangarorin da su ci gaba da su tsaya cak tare da dakatar da duk wani mataki da ya shafi barazanar dakatar da shi ko kuma korar shi daga waɗanda ake ƙara daga na 1 zuwa na 5 har zuwa lokacin da za a saurari karar da aka shigar.

Bayan sauraron lauyan Wike, J.Y. Musa, SAN, Mai shari’a Omotosho ya bayar da dukkanin roƙon da Wike ya nema.

Don haka alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu domin sauraren karar.