Home Labarai Kwalaben kayan maye miliyan 3 matasa maza da mata ke shanyewa a jihar kano – Majalisar Dattawa

Kwalaben kayan maye miliyan 3 matasa maza da mata ke shanyewa a jihar kano – Majalisar Dattawa

0
Kwalaben kayan maye miliyan 3 matasa maza da mata ke shanyewa a jihar kano – Majalisar Dattawa
Cough syrup

 

Kimanin kwalaben magani miliyan 3 ne matasa maza da mata ke shanyewa a tsakanin jihar kano da Jigawa a cewar majalisar dattawa. A yayin da take tattaunawa domin yin dokoki kan yadda matasa maza da mate ke shan kayan maye barkatai.

Dan majalisar dattawa daga jihar Borno, Sen. Baba Kaka Garbai tare da goyon wasu ‘yan majalisar su 37 suka goyin bayan kudurin da zai yi dokar da zata kawo karshen shaye shayen kayan maye da matasa suke yi a fadin kasarnan.

Sanata Barau Jibrin daga kano ne ya tashi domin nuna goyon bayan wannan kuduri. Sanatan yayi Karin bayani inda yace,bincike ya tabbatar musu cewar, da yawan matasan ka shanye kwalba 3 zuwa 8 a kowacce rana na magungunan da ake shad an buguwa.

Ya kara da cewar, kusan yanzu babu wani abu da yake addabar matasa musamman a Arewacin najeriya kamar shan miyagun kayan maye irinsu kodin da sirof da sauransu. Sanatan ya cigaba da cewar, a jihohin Borno ana samun karuwar ayyukan shaye shaye a tsakanin matasa maza da mata, musamman tsakanin wadan day akin Boko haram ya daidaita. In ji sanata Baba kaka garbai.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan batun, Sanata Aliyu Wammako daga Sokoto yace, matsalar shaye shayen kayan maye bata tsaya iyakacin jihohin Arewa ba kadai, yace abu ne day a shafi galibin jihohin kasarnan, dan haka dole ne a yiwa matsalar kallo na tsanaki domin kawo karshenta.

A dan haka ne, majalisar dattawa ta mika lamarin ga kwamatin da ke kula da lafiya da al’amarin amfani da kwaoyi day a duba matsalar, ya kuma zo mata da wata tartibiyar hanyar da za’a shawo kan wannan matsala da ta ke neman kai matasan kasarnan ta baro.

Sannan majalisar tayi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohida na kananan hukumomi da sarakunan gargajiya da kuma kungiyoyi masu zaman kansu domin su tashi haikan domin fadakar da matasa akan irin muguwar ullar da amfani da kayan shaye shay eke haifarwa.

Daga bisani kuma, majalisar tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da cibiyoyin kula tare da canjawa masu fama da shaye shayen tunanin domin saita musu rayuwa wato “Rehabilitation centre” a turance.

Daga karshe shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki, yayi kira ga hukumar hana shad a fataucin miyagun kwayoyi das u tashi tsaye domin yaki da miyagun kwayoyin da matasa ke ta’amali das u. Ya kuma kara jaddada kudurin majalisar ta dattawa wajen ganin ta tsaya kai da fata ganin an yaki dabi’ar shaye shaye a tsakanin matasa.