
Olubankole Wellington, wanda a ka fi sani da Banky W, sanannen mawakin Nijeriya kuma dan majalisar wakilai ta PDP ya ce idan ana son samun ci gaba a Najeriya akwai bukatar a tashi a dena zanga-zanga a tunkari kujerun mulki.
Da yake magana a wata hira da AriseTv, a kan dalilin da ya sa ya shiga siyasa da kuma yin magana kan yakin neman zaben PDP, Banky W ya ce “gaskiya maganar ita ce idan na dace da aikin zane-zane ko dan fafutuka, na kasance ana jin amo na a harkar siyasa. Dole ne mu fara ƙaura daga zanga-zangar zuwa mulki don samun wannan canjin.
Banky W ya zama wanda ya lashe zaben ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar PDP, sannan ya sake tsayawa takara a mazabar tarayya ta Eti-Osa a jihar Legas da kuri’u 24 da 5.