Home Siyasa Mambobin PDP da APC 200 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour a Abuja

Mambobin PDP da APC 200 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour a Abuja

0
Mambobin PDP da APC 200 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour a Abuja

 

 

 

A yau Litinin ne Jam’iyyar Labour Party, LP, a mazaɓar Gaube ta karɓi sama da mutane 200 da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP da APC, a Ƙaramar Hukumar Kuje da ke babban birnin tarayya.

Masu sauya shekar, waɗanda suka miƙa katunansu na jam’iyyar APC, fastoci, tsintsiyoyo da lemomi na jam’iyyar PDP, sun ce matakin ya zama dole domin tabbatar da dimokuradiyya ta gaskiya a kasar nan.

Fanimi Oluwabusayo, babban odita na jam’iyyara birnin tarayya, a lokacin da yake karɓar su, ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta zo ne domin ceto ƴan ƙasa daga halin kuncin da manyan jam’iyyun biyu suka jefa su.

Oluwabusayo, wanda aka fi sani da Biggy, ya ce “Jam’iyyar LP ta zo da cikakken karfi don sauya labarin dimokuraɗiyya a kasar.

“Muna kira gare ku da ku shiga wannan runduna da kawo sauyi mai kyau da kuma ciyar da Nijeriya zuwa wani matsayi mai kyau don kawo karshen talauci da wahala a kasar,” in ji shi.

Abu Tanko wanda ya yi magana a madadin sauran wadanda suka sauya sheƙar ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa ba su gamsu da tsari da manufofin jam’iyyun APC da PDP ɗin ba, shi yasa su ka yanke shawarar barin su.