Home Wasanni Mane ya kammala sauya sheƙa zuwa Bayern Munich da ga Liverpool

Mane ya kammala sauya sheƙa zuwa Bayern Munich da ga Liverpool

0
Mane ya kammala sauya sheƙa zuwa Bayern Munich da ga Liverpool

 

 

 

Bayern Munich, ƙungiyar ƙwallon ƙafa mafi girma a gasar Bundesliga ta ƙasar Jamus, a yau Laraba ta sanar da cewa ta sayi ɗan wasan gaban Senegal, Sadio Mane daga Liverpool kan kwantiragin shekaru uku.

Mane, mai shekaru 30, ya isa Munich ne a jiya Talata don duba lafiyarsa, sannan ya rattaba hannu a kan babbar yarjejeniyar har zuwa 2025.

A yau Laraba ne dai a ke sa ran za a gabatar da Mane a hukumance a gaban magoya bayan kungiyar.

Munich da Liverpool ba su fadi ko nawa ne farashin ɗan wasan ba, amma an kiyasta kudin zuwa yuro wurin zuwa yuro miliyan 32 (dala miliyan 33.7) wanda zai iya ƙaruwar zuwa Yuro miliyan 41 tare da ƙari.

Kyaftin ɗin na Senegal ya koma Liverpool ne a shekara ta 2016 daga Southampton kuma ya lashe dukkan kofunan da kungiyar ta Jürgen Klopp ta lashe s wannan lokaci, inda ya zura mata kwallaye 120 a wasanni 269.

“Mané tauraro ne na duniya, wanda ke jaddada sha’awar FC Bayern kuma zai kara kyawun Bundesliga gaba daya,”