
Dangane da hauhawar farashin kayayyaki da kuma tsadar rayuwa, mata masu juna biyu a fadin Najeriya sun bukaci gwamnati da ta rage wa al’umma raɗaɗin matsin tattalin arziki, musamman ganin yadda farashin magunguna da kayan jarirai ke kara tashin gwauron zabi.
Kimanin mata masu juna biyu 400 ne suka bayyana kokensu a yayin wani taron lafiya da aka gudanar a babban asibitin Ososami, Ibadan, jihar Oyo, domin murnar cikar asibitin shekaru 26 da kafuwa.
Adeloye Titilayo, wacce ta wakilci matan, ta yi kira ga gwamnati da ta magance matsalolin matsin tattalin arziki da iyaye mata masu ciki ke fuskanta.
Ta bayyana tashin kuɗin mota, farashin magunguna, da kayan masarufi, a matsayin babban kalubale, inda ta jaddada muhimmancin suga mata masu juna biyu.
“Dole ne gwamnati ta ba da fifiko wajen samar da kayayyakin aiki a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu. Daƙile tashin kuɗin mota domin mata mata masu juna biyu zuwa asibiti a ranar da aka basu gurbin ganin likita. Saukaka farashin magunguna, abinci mai gina jiki, da kayan abinci na jarirai yana da mahimmanci. Yanayin tattalin arzikin da ake ciki yanzu ya sa waɗannan bukatu ba su da sauƙi ga mutane da yawa, ”in ji ta.
A nata bangaren, Misis Ibironke Omotade, ta jaddada irin dimbin matsalolin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, wadanda ke shafar mata masu juna biyu. Ta bukaci gwamnati da ta aiwatar da tsauraran matakan kawar da talauci tare da inganta ayyukan kiwon lafiya ga dukkan ‘yan kasa.
Dokta Olajumoke Caxton-Martins, Babban Manajan asibitin, ya sake nanata bukatar gaggawar saukin gwamnati, yana mai jaddada muhimmiyar rawa na isasshen abinci mai gina jiki da kiwon lafiya wajen tallafawa lafiyar mata da jarirai.