
Ministan muhalli Ibrahim Usman Jibrin yayi murabus daga kasancewa mamba a majalisar zartarwa ta kasa, hakan ya biyo bayan nada ministan a matsayin sabon Sarkin Nassarawa a jihar Nassarawa.
Ministan ya bayar da takardar murabus dinsa ne, a yayin zaman majalisar zartarwa karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa sabon Sarkin murna tare da bayyana cewar, zabin nasa a matsayin sabon Sarkin Abu ne da ya dace. Yayi masa adduar fatan alheri.