Home Labarai Motar giya ta faɗi daf da ofishin Hisba a Kano

Motar giya ta faɗi daf da ofishin Hisba a Kano

0
Motar giya ta faɗi daf da ofishin Hisba a Kano

 

Wata mota maƙare da katan-katan na giya ta faɗi a daidai ofishin Hisba na Panshekara, Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa kawai gani a ka yi motar, ƙirar Hilux, ta afka cikin kwata.

Bayan da mutane su ka kai agaji ne, sai su ka ga ashe motar barasa ce, inda gurin ya gurmuɗe da tsamin giya.

An dai yi ƙoƙarin zato direban motar wanda ya ji ciwuka, yayin da kwalaben giyar da dama ne su ka faffashe.

Kawo yanzu dai Hisba ba ta ce komai kan batun ba.