Home Siyasa 2023: Mun yi shirin ko-ta-kwana kan yiwuwar zuwa zagaye na 2 a zaɓen shugaban ƙasa — INEC

2023: Mun yi shirin ko-ta-kwana kan yiwuwar zuwa zagaye na 2 a zaɓen shugaban ƙasa — INEC

0
2023: Mun yi shirin ko-ta-kwana kan yiwuwar zuwa zagaye na 2 a zaɓen shugaban ƙasa — INEC

 

Hukumar zabe Mai zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce tuni ta fara tsare-tsare da shirye-shiryen gudanar da zaɓen shugaban kasa zagaye na biyu, inda babu wani dan takara da ya cika sakamakon lashe zaɓen a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kakakin hukumar ta INEC, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a wani taro da shugabanni /editocin na gidajen jaridu a jiya Juma’a a Abuja.

Okoye ya ce irin wannan shiri ya kasance al’adar INEC na duk zaɓukan da hukumar ta gudanar tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya a 1999.

Ya ce tuni INEC ta shirya buga ninki biyu na adadin takardun dangwala zaɓe da ake bukata domin kaɗa kuri’a, idan har ta kama an kai ga zagaye na gaba a zaben.

Ya bayyana cewa, shirye-shiryen su kadai ake yin su tun da fari sabo da hukumar na da kwanaki 21 kacal na gudanar da zabe zagaye na biyu.

Okoye ya ce kafin a ayyana dan takarar a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, dole ne ya samu mafi yawan kuri’un da aka kada, kuma sai ya samu kashi daya bisa hudu na kuri’un da aka kada a kashi biyu bisa uku na jihohin tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce a inda ba a samu wan da ya haɗa wannan adadi ba, tsarin mulki ya ce a gudanar da zabe zagaye na biyu daga cikin ‘yan takarar da ke da kuri’u mafi yawa da rinjaye, kamar yadda sashe na 134, ƙaramin sashe na 2 na kundin tsarin mulki ya tanada.

“Sashe na 134 karamin sashe na 2 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, wanda shi ne tushen dokar kasa, ya wajabta kafin a ce an zabi kowa a matsayin shugaban Tarayyar Najeriya, dole ne dan takarar ya tabbatar da hakan, mafi yawan kuri’un da aka kada a zaben.

“Yanzu, idan babu wani dan takara da ya samu wannan mafi yawan kuri’u da kuma matakin da ya dace, Kundin Tsarin Mulki ya ce dole ne mu sake yin zabe na biyu a cikin kwanaki 21.

“Yanzu, ba duka ƴan takara ne za su shiga wannan zabe na biyu ba. ‘Yan takara 18 ne za su kasance a zaben farko,” in ji shi.