Home Labarai Mutane 19 sun nitse yayin da jiginsu ya kife a kogin Kwara

Mutane 19 sun nitse yayin da jiginsu ya kife a kogin Kwara

0
Mutane 19 sun nitse yayin da jiginsu ya kife a kogin Kwara

A kalla Yara 19 ne suka rasa rayukansu a lokacin da jirgin da suke ciki ya kife kuma ya nitse da su.

Jirgin dai na dauke da Yara 22 a lokacin da suka shiga domin ketare kogin daga kauye Edu a jihar Kwara zuwa wajen wani baki da zasu halarta a jihar Neja.

Dukkan yunkurin da akai na ceto yaran abin yaci tura inda aka ci nasarar tseratar da guda biyu yayin da sauran suka nitse a ruwan.