Home Kanun Labarai Mutum 4 sun mutu, 13 sun ji munanan raunuka a harin ƙunar baƙin wake a jihar Borno

Mutum 4 sun mutu, 13 sun ji munanan raunuka a harin ƙunar baƙin wake a jihar Borno

0
Mutum 4 sun mutu, 13 sun ji munanan raunuka a harin ƙunar baƙin wake a jihar Borno

A ƙalla  mutum hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani harin kunar bakin wake da aka kai a ranar Alhamis a garin Amarwa dake  yankin karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar harin ya faru ne da misalign karfe 2 na rana,a lokacin da wata mata ta layyace jikinta da bamabamai,kuma ta nufi kauyen domin tarwatsa kanta.

Wani wanda abin ya faru akan idonsa, Bukar Fantai, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewar, matar taci nasarar shiga kauyen ne ta hanyar yin basaja a zuwan ita me sayen amfanin gona ce.

Fantai ya cigaba da cewa, matar da farko ta fara nufar wani karamin shagon sayar da kayan masarufi ne, inda ta nemi ta sayar da wasu alawowyi.

Sannan daga bisani, matar ta nufi wata katuwwar inuwa,inda mafiya yawan mutanan kauyen kan zauna a wajen domin hutawa, sannan ta tayar da bom dina wajen.

“Mahariyar ta tayar da bom din da yake layyace a jikinta, inda ta tarwatsa kanta, sannan ta kasha wasu mutum uku nan take, tare da jikkata wasu mutum 13 a lokacin da bom din ya fashe da ita.”

Jami’an tsaro masu lura da kuma kwance bamabamai, sun tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN faruwar wannan al’amari, inda ta kara da cewar, tuni aka garzaya da wadan da suka ji raunuka zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin basu kulawa ta musamman.

Majiyar ta cigaba da cewar, tuni aka tura rundunar ‘yan sanda wajen da abin ya auku, ddomin kawwame wajen da harin ya auku, tare da tabbatar da cewar harkoki sun koma kamar yadda suke a wajen.

Amma dai rundunar sojin Najeriya dake aikin bayar da tsaro a yankin har yanzu bat ace komai ba kan wannan harin.