Home Labarai Nijeriya za ta bai wa daliban Ukraine guraben karatu a jami’o’in gida

Nijeriya za ta bai wa daliban Ukraine guraben karatu a jami’o’in gida

0
Nijeriya za ta bai wa daliban Ukraine guraben karatu a jami’o’in gida

 

 

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta bai wa daliban da yakin Ukraine ya tilasta musu dawowa gida damar karasa karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantun kasar.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin kasashen waje ta kasar ta fitar ta ce tana wani shiri na ganin an sama wa daliban guraben karatu a manyan makarantun kasar.

Ma’aikatar ta ce ta samar da wani form a shafinta na intanet wanda daliban da ke da sha’awar karasa karatu a kasar za su cika.

Dubban daliban Najeriya ne dai aka kwaso daga kasar tun bayan mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine, abin da kuma ke kawo tsaiko ga karatun daliban.

To sai dai ko da sun samu guraben karatun a jami’o’in Najeriya, kammala karatun nasu zai ci karo da tasgaro, sakamakon yajin aikin da malaman jami’o’in kasar ke yi.

Jami’o’in kasar dai sun kwashe watanni a rufe sakamakon yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in kasar ke gudanarwa.