Home Cinikayya NNPC na bin ‘yan kasuwa masu dillancin Mai bashin Naira biliyan 800

NNPC na bin ‘yan kasuwa masu dillancin Mai bashin Naira biliyan 800

0
NNPC na bin ‘yan kasuwa masu dillancin Mai bashin Naira biliyan 800
Maikanti Kachalla Baru

Kamfanin main a kasa NNPC ya bayyana cewar yana bin manyan dillalan man fetur da kungiyar masu safarar man fetur din ta DAPPMA bashin Naira biliyan 800.

Babban sakataren kamfanin na NNPC, Olufemi Adewole ne ya bayyana hakan a wata sanarwa day a fitar a ranar Alhamis, yace amma dole dillalan manfetur din su tabbatar da yunkurinsu na wadata al’ummar kasarnan da man fetur.

Mista Adewole ya kara da cewar, bayan Naira biliyan 600 da NNPC take bin ‘yan kungiyar DAPPMA, sannan kuma, tana bin wasu Karin dillalan man fetur din bashin Naira biliyan 200, wanda a jumlace NNPC na bin su bashin Naira biliyan 800.

“’Yan kasuwa masu dillancin man fetur, sun taimaka wajen wadata al’ummar Najeriya da albarkatun man fetur, duk da bashin da ake binsu na Naira biliyan 600, bayan gashi ana bin sauran ‘yan kasuwarsu wasu Karin kudade day a kai jimillar kudin suka kai biliyan 800” Inji Mista Adewole.

Duk da cewar ‘yan kasuwar basu iya biyan bashin wadancan makudan kudaden da ake binsu bashi ba, amma ‘yan kungiyar dillalan manfetur din suna yin iyakar kokarinsu wajen wadata al’ummar Najeriya da albarkatun man fetur.

Ya kara da cewar, sun fitar da wannan sanarwar ne domin bayyana irin yadda wasu daga cikin ‘yan kasuwar da suke dillancin man fetur din ke yin kokarin wadata al’ummar Najeriya da man fetur, duk da ana cewar sun yi shiru sun kauda kai akan abinda dillalan man fetur din suke yi, musamman a wannan lokacin da aka samu karancin mai a ko ina a fadin Najeriya, wanda NNPC kokaringanin an shawo kan matsalar.

“Wannan sanarwar ba wata tadiya bace ga kokarin ‘yan kasuwar man fetur ko kuma kungiyar wanda sune manyan mataimak ga kamfanin main a kasa domin sadarda albarkatun mai ga sauran al’ummar Najeriya”

“Matsayar NNPC da kuma kokarinta na bayyana irin kokarin da dillalan man fetur suke yi a fadin Najeriya da kuma basu kariya, ba wani abin aibu bane kamar yadda ake ta zargin ana karkata akalar man zuwa ga bukatun wasu daban”.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar 26 ga watan Disamba, ya yi rahoto kan zargin da kungiyar DAPPMA ta yiwa NNPC na kin wadatar das u da man fetur akan lokaci, wanda hakan ya janyo tsaikon da ake samu a wasu tashoshin samar da man fetur din.