
Kwamitin Ƙoli na jam’iyyar PDP ya kama kwamitin riƙo na mutum 13 da za su ja ragamar jam’iyyar.
Matakin ya biyo bayan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yanke a ranar 29 ga watan Agusta, wanda ya tabbatar da ikon jam’iyyar na rusa kwamitocin zartaswa a dukkanin mataka,i tare da naɗa kwamitin riƙo.
A wata wasika mai dauke da kwanan watan Agusta 29, 2022 tare da sanya hannun sakataren kungiyar na ƙasa, Umar Bature, an dorawa kwamitin alhakin tafiyar da al’amuran jam’iyyar a jihar Kano kamar yadda sashe na 21(2) (a-b) na kundin tsarin mulkin jam’iyya ya tanada.
“Muna so mu sanar da ku cewa Kwamitin Koli na PDP na Ƙasa (NWC) na, a madadin kwamitin zartaswa ns kasa, (NEC), bisa ga Kundin Tsarin Mulkin Jam’iyyarmu (2017 kamar yadda aka gyara), ya amince da wanda aka jera a matsayin kwamitin riƙo a Kano, wanda shine, wanda aka rubuta kamar haka,” in ji wasikar.
Ga sunayen ƴan kwamitin
1 ALH. MAI ADAMU MUSTAPHA (Chairman)
2. IBRAHIM A. DAN’IYA (Mamba)
3. ABDULLAHI UNGOGO (Mamba)
4. HON. AMINU A. JINGAU (Mamba)
5. PROF. MUNTARI Y. BANANA (Mamba)
6. BARR. HABIBU ADAMU (Mamba)
7. AUWALU IBRAHIM DAN’ZABUWA (Mamba)
8. ABUBAKAR GWARMAI (Mamba)
9. KABIRU BELLO DANDAGO (Mamba)
10. YAKUBU YAKIMA (Mamba)
11. HAJJI. LADIDI DAN’ GALAN (Mamba)
12. AUWALU MUKHTAR MAIBISCUIT (Mamba)
13. BARR. BABA ALI (Mamba/Sakatariya)
Da aka tuntubi korarren shugaban jam’iyyar, Shehu Sagagi, ya ce ba zai iya cewa komai ba a kan lamarin a halin yanzu.
Sai dai ya ce ya umurci tawagarsa ta lauyoyinsa da su yi nazari a kan lamarin.