Home Rahoto na Musamman RAHOTO: Sama da maniyyata 900 ne za su rasa aikin Hajjin bana a Kano

RAHOTO: Sama da maniyyata 900 ne za su rasa aikin Hajjin bana a Kano

0
RAHOTO: Sama da maniyyata 900 ne za su rasa aikin Hajjin bana a Kano

 

Sama da maniyyata 900, gami da jami’an Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ne za su rasa aikin Hajjin bana sakamakon matsalar rashin jirgin da zai yi jigilar su.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tun da fari, Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta baiwa kamfanin jirgin sama na Azman Air damar jigilar alhazan Kano, su 2,229 zuwa Saudi Arebiya.

Sai dai kuma Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta ƙi amincewa da jirgin Azman a bisa hujjar cewa bashi da girman da zai kwashi alhazai da yawa a lokaci guda.

Wannan na zuwa ne bayan da a ka jibge alhazan, waɗanda su ka fito daga ƙanan hukumomi daban-daban na jihar, a sansanin alhazai tun ranar Asabar ɗin da ta gabata ba tare da an kwashe su zuwa ƙasa mai tsarki ba.

A yau Laraba ne kuma Saudi Arebiya za ta rufe shiga ƙasar domin aikin Hajji, bayan ta ƙara kwana ɗaya a kan ranar da ta sanya za ta rufe bodojinta.

Babban Sakataren hukumar, Muhammad Abba Dambatta, a wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, ya bayyana cewa ya miƙa buƙatar canja jirgin da zai yi jigilar maniyyatan Kano daga Azman zuwa Max Air amma ta ƙi amincewa.

A cewar sa, ya zuwa ranar Litinin ɗin, mamiyyata 900 da wani abu kacal jirgin Azman ya kai Saudiya a sawu 3, lamarin da ya sanya ya nemi agaji da ga NAHCON, wacce ta yi alƙawarin za ta turo jiragen Flynas guda biyu da na Azman guda ɗaya domin kwashe dukkan maniyyatan da kuma jami’an hukumar alhazai ta Kano.

A yau Alhamis, rahotanni sun bayyana cewa jirgin Azman ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda ya kwashi alhazai 250 kacal, inda ya bar sama da 1,000 a ƙasa, har da Shugaban Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano.

Da yake zantawa da manema labarai a safiyar yau Alhamis, Dambatta, ya ce lamarin ya yi matuƙar sanya shi cikin halin damuwa, inda ya dora laifin a kan NAHCON sabo da “gaza cika alkawarin taimakawa wajen kwashe ragowar maniyyatan na Kano.”

Dambatta ya ce a yau, jirgin AZMAN mai daukar fasinjoji 400 zai tashi daga Kano dauke da maniyyata 250 kacal, inda ya bar sama da Maniyata 940 tare da jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jihar.

Dambatta ya kara da cewa Azman Air ya kwashi maniyyata 1,175 a sawu shida sakamakon amfani da suke da ƙananan jiragen da ba su da girman ɗaukar maniyyata masu yawa.

Ya ƙara da cewa “wannan ne ya sa mu ka koka kafin a fara jigilar maniyatan aikin Hajji, ganin cewa muna da mafi yawan alhazai, kuma munyi bayanin cewa mun fi son jirgin kamfanin Max Air ya ɗauki maniyatan Kano saboda yawan maniyatan da mu ke da su.”

Sakataren ya ƙara da cewa sau 11 ya na zuwa shelkwatar NAHCON da ke Abuja a kan wannan batu, ya ƙara da cewa ya rubutawa hukumar wasiƙu sama da 11 don kada a shiga cikin wannan hali, kuma shi ma gwamnan Kano da kansa sai da ya rubuta musu wasika har sau 3 amma abin da aka koka akai sai da ya faru.