
Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi a kungiyar bayan da yanzu ya buga wasa 400 a kungiyar tun bayan da ya koma kulob din daga Manchester United a shekara ta 2009.
Ronaldo, mai shekaru 32 da haihuwa, ya buga wasanne a ranar Talata a wasan da kungiyarsa ta lallasa Borussia Dortmund da ci 3-1 har gida a wasan zakarun turai da suka fafata.
Wannan dan kwallo dai ya buga wasanni 400 dai-dai kenan a Real Madrid sa’annan ya zura kwallaye dari hudu da sha daya a kowanne irin wasa tun bayan komawarsa kungiyar.
Ya kuma taimakawa kungiyar ta lashe gasar zakarun turai sau uku cikin shekaru hudu sannan sun lashe gasar La Liga sau biyu tare da shi sai kuma kofin Super Cup shi ma sau biyu.
Har ila yau dan wasan ya lashe kyautar dan kwallon duniya sau uku a Real Madrid bayan ya lashe guda daya a Manchester United a shekara ta 2009.
Bugu da kari ya jagoranci kasarsa ta Portugal ta lashe gasar nahiyar turai da aka fafata a kasar Faransa a shekarar da ta gabata inda su ka doke masu masaukin bakin daci daya da nema.