
Masana kimiyya na kokarin gano wata kwayar cuta da ta yadu daga dabbobi a gabashin China, inda ta harbi gomman mutane.
An samu kwayar sabuwar cutar wadda aka yi lakabi da Langya henipavirus (LayV) a jikin marassa lafiya 35 a lardunan Shandong da Henan.
Yawancin mutanen da suka kamu da ita suna da alamu na zazzabi da gajiya da tari.
Ana ganin sun dauki cutar ne daga dabbobi, sai dai zuwa yanzu babu shedar da ke nuna cewa za ta iya yaduwa daga wani mutum zuwa wani.
Yawanci masu bincike sun gano kwayar cutar ne a jikin wata dabba mai kama da jaba.
Masanan sun ce a gwaje-gwajen da aka yi an kuma samu kwayar cutar a jikin karnuka da awaki, sai dai ba kasafai ake samunta a jikin nasu ba.
An bayyana labarin bullar cutar ne a wata wasika da masu binciken suka rubuta daga China da Singapore da Australia, wadda aka wallafa a mujallar harkokin lafiya ta New England ta wannan watan.
Sai dai zuwa yanzu bincike bai nuna cewa ko kwayar cutar tana da hadari ba sosai.