
Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo ya yi kira ga al’ummar jihar da kada su bari fafutukar samun shugabancin ƙasa daga kudancin Nijeriya ta fuskanci rashin nasara.
Akeredolu ya ce tun da Arewa ta samar da shugaban kasa tsawon shekaru takwas, to yanzu lokacin da ƴan Kudu ne suma su yi shugabancin kasar.
Ya kara da cewa karbuwar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya samu a fadin kasar nan alama ce ta nasara a zabe mai zuwa.
Akeredolu ya yi wannan kiran ne a wurin gangamin yakin neman zaben Sanatan Ondo ta Arewa na jam’iyyar APC da aka gudanar a garin Owo a jiya Litinin.
Gwamnan ya ba da tabbacin cewa kasar za ta bunkasa a karkashin Tinubu, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Ya bayyana cewa babu wani yarfe da makarkashiya da za su iya dakile nasarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Ya ce yanzu lokacin Tinubu ne na ya yi ya yi mulkin Nijeriya.
“Asiwaju Ahmed Bola Tinubu an gwada shi kuma an amince da shi. Ya taba zama gwamnan Legas kuma mun san yadda ya canza jihar.
“Ina tabbatar muku cewa Najeriya za ta ci gaba a karkashin Tinubu a matsayin shugaban kasa,” in ji shi.