
Muhammad Sanusi Barkindo, sakataren kungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur, OPEC mai barin gado ya rasu.
Barkindo wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tarba shekaran-jiya Litinin, ya rasu ne da misalin karfe 11 na daren jiya Talata.
Mele Kyari, Manajan Darakta na Kamfanin NNPC, ya tabbatar da rasuwar a wani sakon Twitter da ya wallafa a yau Laraba.
“Mun yi rashin mai girma Dakta Muhammad Sanusi Barkindo. Ya rasu ne da misalin karfe 11 na daren jiya 5 ga watan Yuli 2022.
” Tabbas babban rashi ne ga iyalansa, NNPC, kasar mu Najeriya, kungiyar OPEC da kuma al’ummar makamashin duniya. Za a sanar da shirye-shiryen jana’izar nan ba da jimawa ba,” Kyari ya rubuta.
A karshen watan nan a ke sa ran Barkindo zai mika ragamar muƙamin na Sakataren OPEC ga magajinsa a ƙarshen watan nan.