Home Labarai Sama da gidajen burodi 40 sun rufe a Abuja sabo da tsadar kayayyakin aiki

Sama da gidajen burodi 40 sun rufe a Abuja sabo da tsadar kayayyakin aiki

0
Sama da gidajen burodi 40 sun rufe a Abuja sabo da tsadar kayayyakin aiki

 

 

 

 

Aƙalla gidajen burodi 40 ne suka rufe a babban birnin tarayya, FCT, kan tsadar farashin kayayyakin aiki da kuma ƙarin haraji da kuɗin wutar lantarki da dai sauransu.

Wasu gidajen biredi da aka ziyarta ba a buɗe su ba saboda tsadar aiki da haraji da wasu hukumomin gwamnati ke yi.

Wasu daga cikin gidajen burodin da suka rufe shago sun haɗa da Abumme bakery Ltd. Lugbe, titin Airports, Hamdala Bakery, Kuje, Harmony Bite Bakery, Karu, Doweey Delight Bakery Ltd, Kubwa.

Sauran sun hada da Merit Baker, Mpape, Funez Baker, Orozo, Slyz Bakery, Wuse Zone 2, da sauransu.

Ishaq Abdulraheem, Shugaban Kamfanin Biredi na Abuja Master Bakers, FCT, ya bayyana cewa abin damuwa ne ganin cewa gidajen burodin da ke Abuja ba za su iya jurewa tsadar kayan aiki ba.

Ya ce akasarin ‘yan kungiyar sun rasa abin yi, yayin da ma’aikata ma sun rasa aikin yi saboda rufe gidajen burodin da a ka yi.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta shiga tsakani, ta kuma duba hukumomin gwamnati da ke kawo cikas ga harkokin kasuwancin biredi.