Home Labarai Ɗan sanda da ƴan sintiri 5 sun tsere da ga hannun ƴan ISWAP a Borno

Ɗan sanda da ƴan sintiri 5 sun tsere da ga hannun ƴan ISWAP a Borno

0
Ɗan sanda da ƴan sintiri 5 sun tsere da ga hannun ƴan ISWAP a Borno

 

Rundunar ƴan sanda a jihar Borno ta tabbatar da tserewar jami’an tsaro shida da ƴan ta’addar ISWAP su ka yi garkuwa da su a garin Benishek a ranar Litinin.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Abdu Umar ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da jami’an ‘yan sanda reshen jihar a jiya Laraba a Maiduguri.

“Yan ta’addan sun yi awon gaba da jami’an tsaro shida da suka hada da dan sanda daya, da ƴan sintiri wato CJTF uku da mafarauta uku.

“Sun kuma ƙwace motar sintiri, kirar Hilux guda ɗaya, sannan mun kuma yi asarar bindiga kirar AK 47 guda daya.

“Amma tare da gudunmawar rundunar sojojin sama, jami’an tsaron sun samu nasarar tserewa bayan da maharan suka tsere cikin daji suna ganin jiragen yaƙin Super Tucanos,” in ji shi.